TAFIYAR MU GIDAJEN TARIHI

Mawaki/Marubuci: Abdulhakim Dayyabu (CEO AHD Clothing)

Tafiyar mu ta fara karfe tara
Mun shiga cikin doguwar mota fara
Muka zauna kamar yadda aka tsara
Da ga nan masu magana suka fara
Muka natsu muna saurara
Ba dadewa ba jira
Akayi addu’a tare da kabbara

Sai muka hau hanya
Muka cigaba da tafiya
Sai gamu a hasumiya
Ta Gobarau kaji ginin jiya
Aka yi bayanai hadda su tambaya
Muka hau sama duk muka zagaya
Akayi raha aka sha dariya

Daga nan ba kakkautawa
Muka kama hanyar wata unguwa
Kofa Uku tafi misaltuwa
Nan da nan Allah yai mana isowa
Muka sauko muna takawa
Muna shiga muna zagayawa
Muka sha bayanai tun daga sayawa
Mu kau muka rinka tafawa

Akayi hotuna aka dada aka kara
Muka fito aka hada mu da gara
Ka san Katsinawa akwai kara
Daga nan muka dauki hanyar Daura

Muka sha bayanai na basira
Daga mutane masu baiwa da fikira
Haka kuma anyi allura
Akan wasu muhimman al’amura

Sai gamu a Daura ba makara
Mu shiga aka kara cin gara
Akasha akaci aka kakkara
Akayi yi Sallaloli bayan kabbara

Aka koma kuma aka saurara
Bayanai na tarihi suka yi ta kwarara
Daga bakin Wakilin Daura
Na tarihi kunji na kara
Kai abun sai dai an saurara

Muka zarce kai tsaye karara
Zuwa rijiyar kusugu ta garin Daura
Akaja akasha aka kakkara

Muka hau mota ba wani jira
Muka isa Kofar Bayajiddan Daura

Daga karshe dai muka sha fura
Muka sha bayanai muka sha fira

Allah dai ya saka da gidan tsira
Ya saka da alheri duniya da lahira

Write a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Share via
Copy link
Powered by Social Snap